Ra’ayi riga… Bilyaminu ya gamu da abun da ya kamace shi don shi mayaudari ne – inji kawar Matar shi

Maryam tace Bilyaminu ya samu abun da ya kamace shi domin shi kasurgumin mayaudari ne.

Wata kawar Maryam Sanda wanda ake zargi cewa ta kashe mijinta ta mara mata baya bisa ga zargin da ake mata.

Kawar mai suna Maryam Aliyu ta wallafa a shafinta na facebook ra'ayin ta game da al'amarin da ya faru tsakanin dan tsohon shugaban jam'iyar PDP mai suna Bilyaminu Muhammed Bello da matar sa Maryam Sanda wanda batun su ya tada kura a fadin kasar.

 

Maryam tace Bilyaminu ya samu abun da ya kamace shi domin shi kasurgumin mayaudari ne.

Yar asalin karamar hukumar kangiwa dake nan jihar Kebbi ta nuna alamun goyon bayan Maryam Sanda kuma ta bayyana dalilai da zai sa mutane su daina zargin Maryam Sanda da aikata laifin.

"Bilyaminu Kasurgumin mayaudari ne kuma ya gamu da abun da ya kamace shi.

Mutane na ta korafi akan batun Bilyaminu da Maryam ba tare da sun san hakikanin abun da ya faru.

 

Babu wata kwakwarar shaida mai nuna cewa ita ta aikata laifi. Abun da na sani shine shi dai kasurgumin mayaudari ne kuma a ra'ayi na ya gamu da abun da ya kamace shi.

Idan ma Maryam ta kashe shi wanda na san ba haka bane, ai tayi  dai dai domin yana yaudarar ta da bin mata ba tare da ta sani ba.

Ni dai na tsaya a bangare mai  cewa ya mutu ne yayin da suke rigama amma ba wai ta kashe shi da hannun ta. Ki cigaba da juriya Maryam, Allah yana tare da ke." Kamar yadda ta wallafa a shafinta.

READ  Super eagles: FIFA ta sauya sakamakon wasan Nijeriya da Algeria tare da hukunta NFF na biyan tara

Karanta labarin Yan sanda sun gano bidiyo mai nuna yanda abubuwa suka kasance kafin mutuwar Bilyaminu

A safiyar ranar lahadi 19 ga watan Nuwamba ne labari ya barke mai nuna cewa Maryam ta caccaki mijinta da wuka bayan wata sakon waya da ta gani hirar sa da wata mace.

Mauratan wadanda aka daura auren su cikin shekarar 2015 sun samu 'ya mace yar wata takwas albarkacin auren su.

[source: http://www.pulse.ng/hausa/raayi-riga-bilyaminu-ya-gamu-da-abun-da-ya-kamace-shi-don-shi-mayaudari-ne-inji-kawar-matar-shi-id7638725.html]

%d bloggers like this: